Shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma a ranar Alhamis din nan ya sanar da cewar, za'a bude makarantun a ranar 30 ga watan Maris mai zuwa a duk fadin kasar, wadanda aka rufe su sakamakon barkewar cutar Ebola.
A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, Mr Koroma ya riga ya nada tsohon kwamishinan zaben kasar a matsayin jami'i mai gudanar da ayyukan yau da kullum na tsari da aiwatarwar duka abin da ya dangancin komawa makarantu kuma ita ke da alhakin ba da rahoton ga shugaban kasar.
Shugaban kasar na Saliyo ya kuma ba da amincewa a hukumance na fara duk ayyuka da suka hada da wayar da kan jama'a, tsabtace ruwan sha da muhalli, ababen bukata na tsabtar jiki da kuma walwalar al'umma da ba da goyon bayansu wajen ganin an bude makarantun a watan Maris. Wannan sanarwar ta gwamnatin ta fara aiki nan take.
Iyayen yara da Xinhua ta yi hira da su sun yi maraba da wannan sakamako amma suna da ra'ayin cewa, gwamnati ta jira sai an tabbatar da cewa, cutar ta bar kasar baki daya.
Kakakin gwamnati a nasa bangaren ya yi bayyanin cewar, mahukunta sun rika sun lura da hakan, amma shawarar sake bude makarantun ta biyo bayan kasa sosai da yaduwar cutar ta yi a kasar. (Fatimah)