in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar likitoci Sinawa da ke Laberiya tana jinyar wata mace da ta kamu da cutar Ebola
2015-02-02 11:04:41 cri
A ranar Asabar ne kungiyar likitocin kasar Sin ta biyu dake kasar Laberiya ta tabbatar da cewa, matar da take kula da ita ta kamu da cutar Ebola, wadda ta kasance wadda ta kamu da Ebola ta farko da kungiyar Likitocin kasar ta Sin ta karba, bayan da kungiyar ta fara aiki a yankin da ake fama da cutar Ebola.

A cewar Zhang Yong, darektan sashin binciken majiyyata na cibiyar kula da wadanda suka kamu da cutar Ebola da kasar Sin ta kafa a kasar Laberiya, majiyyaciyar tana da shekaru 49 da haihuwa, wadda ta fara rashin lafiya a makon da ya gabata, daga bisani alamun cutar suka kara bayyana. An ce, cikin iyalin majiyyaciyar akwai wani da ya mutu cikin kwanaki 10 da suka wuce sakamakon cutar Ebola.

Bayan da aka tabbatar da matar da ke jinya ta kamu da cutar Ebola, likitocin kasar Sin sun kaddamar da shirin ko ta kwana nan take, ta yadda aka gabatar da wani shirin jinya a matakin farko. A cewar Yang Haiwei, shugaban kungiyar likitocin kasar Sin, za a yi iyakacin kokari don jinyar matar,ta yadda za a warkar da ita nan da nan. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China