A kokarin da ake na kara karfin ayyukan MDD, da gudanar da ayyukan hana yaduwar cutar Ebola, ba da jinya ga masu kamu da cutar, da yin rigakafin cutar ne, aka kafa tawagar MDD ta musamman kan yaki da cutar a watan Satumba na bara. Wannan shi ne karo na farko da MDD ta kafa wata tawagar tinkarar matsalar da ta shafi kiwon lafiya, kuma cibiyarta na birnin Accra dake kasar Ghana.
Kaba tana fatan kasashen duniya, ciki har da kasar Sin za su ci gaba da ba da gudummawa ga kasashen yammacin Afirka har zuwa lokacin da za a kawo karshen cutar ta Ebola. Kaba ta kuma bayyana cewa, Sin tana iya taimakawa kasashen yammacin Afirka masu fama da cutar Ebola, ta yadda za su sake inganta matakansu na kiwon lafiya, musamman a kasashen Saliyo da Liberia, da kuma kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen a fannin kiwon lafiya bayan da aka kawar da cutar don kara inganta karfinsu na tinkarar cututtuka masu yaduwa a nan gaba. A cewarta, Sin ta taba samun sakamako a wannan fanni. (Zainab)