in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar UNDP za ta fara ziyarar kasashen da suka yi fama da Ebola
2015-02-13 11:05:15 cri

Babbar jami'ar hukumar ayyukan ci gaba ta MDD UNDP Helen Clark za ta fara ziyarar aiki a kasashe uku da suka yi fama da cutar Ebola, da suka hada da Guinea, Liberiya da Saliyo tun daga ranar 11 zuwa 18 na wannan watan Fabrairu domin tabbatar da goyon bayan MDD wajen shawo kan wannan matsala da ake fuskanta, da kuma taimakawa na ganin ana samun saukin ta kamar yadda wata sanarwar majalissar ta bayyana.

A lokacin ziyararta a kasar Liberiya tsakanin ranar 13 zuwa 16, jami'ar MDD za ta gana da shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf, ma'aikatan MDD, ma'aikatan kula da ayyukan dakile cutar, da kuma kungiyoyin ba da taimako, sannan ana sa ran za ta halarci bikin rattaba hannu na wani shirin aika sakonnin kudade mai ba da kariya tsakanin ofishinta da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Liberiya da za'a yi a gundumar Bomi.

Sanarwar majalissar ta bayyana cewa, illar da wannan cuta ta kawo a harkokin walwala da tattalin arzikin al'umma za ta dade kafin ta dawo daidai ko da bayan an dakile wannan cuta wadda ta kawo matsin rayuwa ga mafi talauci da rashin galihun al'umma a wadannan kasashen.

A martanin game da bukatar da gwamnati ta bayyana na son a fara aiwatar da shirin da za'a yi bayan dakile cutar tare da ayyukan da ake na dakile ta gaba daya a lokaci daya, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya umurci jami'ar majalissar ta jagoran wannan shirin na majalissar game da ganin karshen cutar.

Hukumar ta UNDP tana aiki ne tare da hukumomin gwamnatocin kasashe da kananan hukumomi, yankuna da kungiyoyin kasashen waje a kan tantance ayyukan warka daga cutar, in ji sanarwar majalissa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China