Shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe, kana mai kula da harkokin gamayyar kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) domin ba da amsa mai kyau kan matsalar cutar Ebola, ya tabbatar wa shugaban kasa da al'ummar Saliyo cewa, gamayyar ta bullo da wasu dabaru domin baiwa kamfanonin jiragen sama damar maido da harkokin zirga zirgarsu zuwa wannan kasa.
Shugaban Togo ya ba da wannan tabbatanci ne a makon da ya gabata a yayin wani rangadin aiki da ya kai a kasar Saliyo da sauran kasashen da cutar Ebola ta galabaita. Mista Gnassingbe ya bayyana goyon bayansa ga al'ummar kasar Saliyo, tare da tabbatar musu da cewa, kasarsa za ta sanya duk wani kokarin da ya dace domin ganin an dauke wannan hani na zuwa Saliyo daga wajen kamfanonin jiragen sama.
Kimanin kamfanonin jiragen sama bakwai da ke gudanar da sufurinsu zuwa kasar Saliyo, da suka hada da British Airways, Kenya Airlines da kamfanonin jiragen saman kasar Faransa, suka dakatar da zuwa kasar Saliyo tun bayan barkewar cutar Ebola a wannan kasa.
Shugaban kasar Togo, ya bayyana cewa, kungiyar ECOWAS ta bullo da wasu matakai domin fuskatar matsalolin na bayan Ebola, da mai da hankali wajen karfafa harkokin kiwon lafiyar jama'a a cikin shiyyar ECOWAS, ta yadda za'a samu zarafin murkushe duk wani sabon kalubalen kiwon lafiya a nan gaba. (Maman Ada)