Mwencha wanda ya bayyana hakan a hedkwatar kungiyar ta AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha, ya kara da cewa, baya ga samar da kudi, da magunguna, da na'urori ga kasashe masu fama da cutar Ebola, kasar ta Sin ta kuma aike da likitoci zuwa wadannan kasashen, domin taimakawa wajen yaki da cutar ta Ebola.
Kana Mwencha ya ce, a halin da ake ciki, an samu ci gaba a yakin da ake yi da cutar ta Ebola a kasashen yammacin Afirka, sai dai duk da haka akwai bukatar karin lokaci, kafin a kai ga shawo kan cutar baki daya a wannan karo.
Haka zalika, Mwencha ya ce yayin taron koli na kungiyar AU karo na 24, wanda za a gudanar a ranar 30 zuwa 31 ga wannan wata, za a tattauna game da kafa cibiyar rigakafi, da yaki da cututtuka ta Afirka, a wani mataki na tabbatar da hana yaduwar cutar ta Ebola. (Zainab)