Likitocin kasar Sin sun fara wannan aiki ne bisa rokon ma'aikatar lafiya ta kasar Saliyo, wadda ta bukaci likitocin da su fara binciken kwayoyin cutar Malaria tare da na cutar Ebola a ranar Asabar 7 ga wata, sa'an nan za su mika duk sakamakon da suka samu ga hukumomin kasar a kai a kai.
A cewar Fang Tongyu, shugaban tawagar likitocin kasar Sin, a kan yi binciken jinin mutane kimanin 200 a ko wace rana a kasar ta Saliyo, sa'an nan a mako guda da ya wuce, yawan mutanen da aka gano dauke da cutar Ebola a ko wace rana bai wuce 20 ba, hakan na nuna cewa yanayin bazuwar cutar Ebola na raguwa a kasar, kuma sannu a hankali za a kawo karshenta.
Tun da likitocin kasar Sin masu kula da aikin binciken cututtuka da dakin gwaji na tafi-da-gidanka suka isa kasar Saliyo a watan Satumba da ya wuce, ya zuwa yanzu sun riga sun gudanar da bincike kan jinin mutane 4272, daga cikinsu 1416 suka kamu da cutar, kana binciken da likitocin kasar Sin suke yi a wannan kasa ya cimma nasara sosai, ba su taba yin kuskure ba. (Bello Wang)