Shirin wanda aka kaddamar a jiya Jumma'a dai zai maida hankali ne ga wayar da kan jama'a, game da illar dake tattare da ayyukan ta'addanci, da kuma barazanar da tashe-tashen hankula ke haifarwa.
Da yake yiwa manema labaru, da sauran masu ruwa da tsaki karin haske game da shirin, babban mashawarcin shugaban kasar kan harkokin tsaro Sambo Dasuki, ya ce kungiyar tarayyar Turai ta EU, da wasu hukumomin kasa da kasa ne za su dauki nauyin shirin.
Dasuki ya ce karkashin wannan shiri, za a fadada ayyukan wayar da kan jama'a, game da matakan da gwamnati ke dauka a wannan fanni, ciki hadda matakan hana karkatar da kwakwalen jama'a, da baiwa masu tada kayar baya damar fita daga kungiyoyin ta'adda, da kuma sauran matakan yada muhimman bayanai tsakankanin al'umma.
Kazalika mashawarcin na shugaban Najeriya, ya ce za a rika tattara bayanai game da mabiya darikun addinai daban daban, da kididdigar yawan su, da wuraren ibada, tare da tantance irin akidun da ake yadawa mabiya. Ya ce ma'aikatar tsaron kasar za ta shigar da wasu sassanta, da suka jibanci harkokin fararen hula cikin shirin, domin tabbatar da nasararsa. (Saminu Alhassan)