in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 32 suka mutu ,47 suka ji rauni a fashewar bam guda biyu na Jos
2014-12-12 21:02:50 cri
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewar yanzu haka mutane 32 ne suka mutu sannan wadansu 47 suka ji rauni sakamakon fashewar bam har sau biyu a garin Jos na jihar Filato dake arewacin kasar a yammacin ranar alhamis din ann.

Babban jami'i mai kula da hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA Abdulsalam Mohammaed ya shaida ma manema labarai a ranar jumma'an nan cewa an riga an kai gawawwakin wadanda suka mutu dakin ajiye su a asibiti.

Abdulsalam Mohammed yace mutane 47 kuma da suka ji rauni suna karban jinya a asibitn kwararru na jami'ar Jos,asibitin kwararru na jami'ar Bingham da kuma asibitin our lady of apostle duka a cikin garin na Jos.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China