Tun a ranar Jumma'a 6 ga watan Febrairu, yankunan Bosso da Diffa na kasar Nijar suka fara fuskantar jerin hare hare daga mayakan kungiyar daga sansanoninsu dake Najeriya, da ma tashe tashen boma bomai daga 'yan ta'addan a birnin Diffa da kewayensa a makwannin da suka gabata.
Hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 15 a bangaren jami'an tsaro na FDS, a yayin da aka kashe mayakan Boko Haram kusan 280 kana aka cafke wasu kimanin 160.
Yau kusan mako ke nan, zaman lafiya ya dawo a birnin na Diffa tare da taimakon jami'an tsaro na FDS dake sintiri dare da rana.
A lokacin, da yake jawabi ga bangaren jami'an tsaron kasar Nijar da suka shiga yaki da Boko Haram, shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou yayi alkawarin cewa za su ci nasarar wannan yaki domin a cewarsa, sojojin sun kware wajen yaki kuma sun zabi sana'ar aikin soja, domin su sojoji ne masu juriya da kwazo kana kuna alfahari da aikinku, kuma kuna karkashin ofisoshin da suka nuna kwarewa kan ayyukansu a fagen daga a kasar Nijar da ma ketare.
A yakin da sojojin Nijar suke yi da Boko Haram a kudu maso gabashin Nijar, suna samun taimakon sojojin kasar Chadi, Amurka da kuma sojojin musamman na kasar Faransa. (Maman Ada)