in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya na kara samun nasara a yakin da suke yi da dakarun Boko Haram
2015-02-20 16:31:48 cri

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta na ci gaba da samun galaba a yakin da take yi da dakarun kungiyar nan ta Boko Haram.

Hakan a cewar kakakin ma'aikatar tsaron kasar Chris Olukolade, ya biyo bayan hare-hare ta sama da sojojin ke kaiwa sansanonin kungiyar dake sassan arewa maso gabashin kasar.

Chris Olukolade, ya ce sojoji sun hallaka mayakan kungiyar da dama ya yin luguden wuta da suka yi kan maboyar 'yan Boko Haram dake dajin Sambisa da wani yanki na Gwoza duka a jihar Borno.

Ya ce an samu cikakkiyar nasara a farmakin baya bayan nan da sojoji ke gudanarwa, koda yake bai hakikance yawan wadanda aka hallaka a hare-haren na wannan lokaci ba.

Kafin hakan a Larabar da ta gabata, ma'aikatar tsaron Najeriyar ta fidda wata sanarwa dake cewa an hallaka mayakan Boko Haram sama da 300 a jihar Borno cikin 'yan kwanakin nan, kana sojoji sun kwace makaman yaki da dama, baya ga mayakan kungiyar masu yawa da aka cafke.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China