in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta saki mutane 158 da ta yi garkuwa da su
2015-02-20 20:25:36 cri
Rahotannin baya bayan nan na cewa kungiyar Boko Haram, ta saki wasu mata da kananan yara su 158, wadanda ta yi garkuwa da su daga kauyen Katarko na jihar Yobe dake Arewa maso Gabashin Najeriya.

Da yake tabbatar da aukuwar wannan lamari, kwamishinan ma'aikatar shari'ar jihar ta Yobe Ahmed Goniri, ya ce an saki mutanen ne bayan sun shafe makwanni 3 a tsare. Goniri ya ce tuni wasu daga wadannan mutane da suka samu kubuta suka sadu da 'yan uwansu.

Kwamishinan shari'ar, wanda kuma ke jagorantar kwamitin lura da wadanda rikicin Boko Haram ya ritsa da su, ya kara da ce gwamnatin jihar na tantance matsayin wadannan mutane, ya yin da a hannu guda ake samar musu da tallafin kula da lafiya domin su samu nutsuwa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China