in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Nijar ta amince da tura dakarunta don yaki da Boko Haram
2015-02-10 20:14:24 cri

A jiya ne majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta amince baki dayanta da tura sojojin kasar zuwa Najeriya tare da sauran dakaru daga kasashe makwabta don yaki da mayakan Boko Haram.

Wannan mataki da majalisar ta dauka ya zo ne a dai-dai lokacin da yankunan Bosso da Diffa da ke gabashin kasar ta Nijar wadanda ke makwabtaka da Najeriya suka fuskanci hare-haren mayakan Boko Haram a ranar Jumma'ar da ta gabata.

A jawabinsa kakakin majalisar dokokin kasar ta Nijar Hamadou Salifou ya ce, amincewar da majalisar ta yi ta tura sojojin kasar don yaki da Boko Haram za ta taimaka wajen samar da tsaro ga al'ummar kasar, nuna goyon baya ga Najeriya tare da amsa kiran da kungiyar tarayyar Afirka wato AU ta yi na kafa rundunar shiyya da za ta yaki mayakan na Boko Haram.

Kundin tsarin mulkin Nijar ya tanadi cewa, wajibi ne gwamnatin ta nemi iznin majalisar kafin ta tura dakarun tsaro zuwa wani aiki a wajen kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China