in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane kusan 21 aka kashe a cikin wasu sabbin hare haren Boko Haram a arewacin Najeriya
2015-02-21 16:57:15 cri
A kalla mutane 21 aka kashe a ranar Jumma'a a yayin da mayakan kungiyar Boko Haram suka sake kaddamar da hare hare kan wasu kayuka uku da ke jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, a cewar wasu mutanen da lamarin ya faru gaban idonsu.

Mambobin wannan kungiyar ta'addanci sun mamaye kayukan da ke kusa da birnin Chibok, da ke kudancin jihar Borno, inda kungiyar ta Boko Haram ta sace dalibai mata fiye da 200 yau kusan watanni goma da suka wuce.

Mayakan sun harba bingigo a kai a kai, in ji wani mazaunin birnin Chibok, Daouda Ali da lamarin ya faru gaban idonsa a cikin wata hira ta wayar tarho tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China