Sojojon Najeriya sun karfafa ayyukansu kan sansanonin kungiyar Boko Haram dake arewa maso gabashin kasar bayan sun kashe mayakan kungiyar da dama, in ji kakakin rundunar sojojin kasar a ranar Litinin. Chris Olukolade, kakakin rundunar sojan Najeriya, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, sojojin Najeriya sun kammala aikinsu na kawar da 'yan ta'addan Monguno da kewaye a wannan safiya.
A cewar mista Olukolade, sun cafke wasu 'yan ta'adda tare da kama wata motar dakon kaya shake da shimkafa, da hatsi da sauran kayayyaki na bukatun 'yan ta'addan dake kai hare-hare a kewayen Baga a yayin wannan samame. Haka kuma jami'in sojan ya kara da cewa, ana ci gaba da kai hare-hare ta sama da ta kasa bisa wani yunkurin kara dannawa gaba zuwa sauran yankunan dake hannun kungiyar Boko Haram. (Maman Ada)