in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECCAS ta amince da samar da tallafi domin yaki da kungiyar Boko Haram
2015-02-17 10:17:13 cri

Shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin tsakiyar Afirka ta ECCAS, sun amince da wani kuduri na samar da tallafin kudi, har kimanin dalar Amurka miliyan 100 domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Rahotanni sun ce, shugabannin kasashen kungiyar 6, da sauran wakilai mahalarta sun rattaba hannu kan sanarwar Yaounde gabanin kammalar taron, wadda ke kunshe da bukatar kara hada gwiwa wajen yakar ayyukan ta'addanci. Kaza lika sun amince da bukatar hada karfi da kungiyar ECOWAS domin cimma nasarar hakan.

Taron ya kuma yi kira ga sauran kasashen duniya, da su kara ba da nasu tallafi, a yakin da ake yi da dakarun kungiyar ta Boko Haram.

Kwarya-kwaryar taron wanda ya kammala a jiya Litinin, ya samu halartar shugaba Paul Biya na Kamaru, da Idriss Deby Itno na Chadi, da na Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo. Sauran sun hada da shugaban kasar Gabon Ali Bongo, da na Congo Deniss Sassou Nguesso, da kuma shugabar rikon kwaryar Afirka ta Tsakiya Catherine Samba-Panza. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China