Kwamitin sulhu na MDD ya nuna cewa, dukkanin ire-iren ta'addanci, ciki hada da Boko Haram su kasance daya daga cikin kalubaloli mafi tsanani ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa.
Haka kuma, kwamitin ya jaddada cewa, yana tsayawa tsayin daka domin yaki da ta'addanci bisa kundin tsarin MDD, ya kuma jaddada cewa, ya kamata a gurfanar da wadanda suka aikata shi, shirya shi ko samar da kudade ga ayyukan ta'addanci gaban kuliya, a sa'i daya kuma, kwamitin ya bukaci kasashen da abin ya shafa su dauki alhakinsu yadda ya kamata bisa dokokin kasa da kasa da kuma kudurorin kwamitin sulhu na MDD da abin ya shafa, da kuma hada kai da bangarori daban daban kan aikin yaki da ta'addanci cikin himma da kwazo. (Maryam)