Da yake karin haske game da hakan, kakakin ma'aikatar tsaron Najeriyar Chris Olukolade, ya ce cikin kwanaki biyu da sojojin suka kwashe suna artabu da 'yan Boko Haram din, sun samu nasarar kwace nau'o'in kayan fada daban daban daga gare su. Sai dai ya ce sojoji 2 sun rasa rayukan'su, yayin da kuma wasu 10 suka jikkata a fagen daga.
Wannan dai mataki na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Chadi, da Kamaru, da Nijar suka amince suyi hadin gwiwa da Najeriya, wajen yaki da kungiyar ta Boko Haram, kungiyar da ayyukanta suka haddasa kisan akalla mutum kusan 13,000 tare da raba wasu sama da miliyan guda da gidajen su.
A wani ci gaban kuma, shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, ya fidda wani sabon faifan bidiyo a jiya Talata, wanda ta cikin sa yake shaida aniyar kungiyar sa ta hana gudanar zabukan kasar dake tafe. Sakon na Shekau dai na zuwa ne jim kadan, bayan wasu hare-haren kunar bakin wake biyu da ake dangantawa da kungiyar, sun hallaka mutane 38 a Arewa maso Gabashin kasar.