in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeriya ta fatattaki mayakan boko haram daga garin Baga a jihar Borno
2015-02-22 16:17:35 cri
A ranar Asabar din nan Rundunar tsaron Nigeriya dake arewa maso gabashin kasar ta sanar da cewa a safiyar jumma'a da yawan 'yan kungiyar boko haram sun nutse a tabkin chadi lokacin da suke guje ma luguden wutan da sojojin Nigeriya suka kai masu lokacin da suke kokarin shiga garin Baga na jihar Borno.

Kamar yadda kakakin rundunar tsaron kasar Manjo Janar Chris Olukolade ya bayyana cikin wata sanarwa da Xinhua ta samu, ya ce an kai ma 'yan kungiyar samame ne ta jiragen saman yaki abinda ya kawo masu ciksa na karasawa cikin garin na Baga yasa suka nemi tserewa ta ruwa.

Yace duk da kokarin da 'yan kungiyar suka yin a dasa nakiyoyi a fiye da wurare 1500 a kan hanyar zuwa garin ba hana aka dakatar da su tare da fatattakar su ba.

A cewar Janar Olukolade, duk wadannan nakikoyi an samu nasarar cire su daya bayan daya cikin dabarar kwararru, sannan yace da daman su sun halaka sannan wassunsu kuma sun tsere da raunuku masu girma a lokutan da aka dinga dauki ba dadi dasu a kokarin dakarun sojin Kasar na shiga garin na Baga.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China