in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira ga rundunar sojojin Najeriya da ta taka rawar a zo a gani wajen yaki da Boko Haram
2015-02-14 16:11:32 cri
Babban jami'in MDD dake kula da yammacin Afrika ya yi kira a ranar Jumma'a ga wani mataki mai kyau da sakamako mafi mahimmanci daga wajen rundunar sojojin Najeriya a yayin da suke gudanar da ayyukan hadin gwiwa tare da kasashe makwabta wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Mohammed Chambas, wakilin musamman na sakatare janar na MDD Ban Ki-moon kana darektan cibiyar MDD dake kula da yammacin Afrika (UNOWA), ya kuma amince da matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Najeriya ta dauka na dage zabukan Najeriya na wannan mako zuwa karshen watan Maris, tare da yin kira ga hukumar da ta baiwa dukkan 'yan Najeriya damar jefa kuri'unsu a yayin wadannan zabuka, tare da yin kira ga jami'an tsaron kasar da su tabbatar da tsaron zabe cikin 'yanci da gaskiya.

Muna jiran sojojin Najeriya suka kara himmatuwa, in ji mista Chambas a gaban 'yan jarida a cibiyar MDD dake birnin New York da hanyar wata hirar bidiyo tun daga birnin Abuja, hedkwatar kasar Najeriya. Mun ga yadda suka yi aiki cikin sahihanci a wasu yankunan duniya. Sun taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya baki daya tun yau da shekaru da dama kuma sun nuna kwarewa.

Muna fatan ganin wannan kwarewa tasu da kwazonsu wajen yaki da Boko Haram, in ji mista Chambas.

Shugaban kasar Nijeriya, Goodluck Jonathan da jam'iyyun adawa sun amince dukkansu da gusa zabukan.

Muna fatan bayan zabukan, 'yan Najeriya za su samu damar hada kansu wajen yaki da Boko Haram, kuma a shirye muke wajen ganin wani babban mataki daga wajen rundunar sojojin Najeriya, ta hanyar samun sakamako mafi mahimmanci wajen yaki da Boko Haram, in ji Mohammed Chambas. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China