in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi allah wadai da harin da aka kai a arewacin Najeriya
2014-12-01 20:09:03 cri
Kasar Sin ta yi allah wadai da kakkausar murya kan harin bam din da aka kai ranar Jumma'a a babban masallacin Jumma'a na birnin Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ya haddasa mutuwar a kalla mutane 120 kana sama da 270 suka jikkata.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ce ta bayyana hakan a yau yayin taron manema labarai, inda ta ce, kasar Sin tana allah wadai da wannan hari tare da kin amincewa da duk wani nau'i na ta'addanci.

Ta kuma yi amfani da wannan dama wajen mika sakon ta'aziya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.

Hua ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan kokarin da Najeriya ke yi na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China