in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da harin da aka kai a masallacin dake Najeriya
2014-11-29 16:58:41 cri

Babban magatakardan MDD Mr Ban Ki-Moon ta bakin kakakinsa a ran 28 ga wata, ya yi kakkausar suka ga harin da aka kai a wani masallacin dake kasar Najeriya.

Sanarwar ta bayyana cewa, Mr. Ban ya yi kira ga mahukuntan kasar Najeriya da su gurfanar da wadanda suka aikata laifi a gaban kuliya ba tare da bata lokaci ba, tare da nanata cewa, duk wani harin da aka kaiwa fararen hula babban laifi ne. Ban da haka kuma, ya jajantawa iyalan mamata da gwamnatin kasar, kuma yana fatan samun sauki ga wadanda suka ji rauni. A karshe kuma, Mr. Ban ya jaddada niyyar MDD na goyon bayan kokarin da Najeriya ta yi wajen yaki da ta'addanci. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China