An ba da labari cewa, wasu dauke da makaman da ba a san ko su wane ba sun ta da boma-bomai uku a cikin wannan masallaci, daga baya kuma, suka yi luguden wuta kan fararen hula dake neman tsirar da rayukansu. Jiya 25 ranar Juma'a ce, musulmai sun je sallar jumma'a, dalilin hakan ya sa harin ya janyo asarar mutane da dama. 'Yan sandan birnin Kano sun shedawa manema labaru cewa, mutane a kalla 35 sun rasa rayukansu a a wannan harin.
Har wa yanzu, babu wata kungiya ko daidaikun mutane da suka sanar da daukar alhakin wannan harin, amma ana zargin kungiyar Boko Haram na da hannu cikin lamarin.
Boko Haram ta rika kai hare-hare irin wannan a cikin watani da dama da suka shude a arewacin kasar Najeriya. Bisa kididdigar da gwamnatin kasar ta bayar, an ce, yawan mutane da suka mutu sakamakon hare-haren 'yan ta'adda a wannan shekara ya haura 1500. (Amina)