An ba da labari cewa, Sin ta samu ci gaba sosai a wannan fanni a shekarun nan da suka gabata, domin ganin dokoki da ka'idoji da tsare-tsare masu inganci da aka kafa game da wannan batu. Duk da haka, saboda yawan kauyuka da kasar ke da su kwarai, ba a iya aiwatar da wannan aiki sosai a duk fadin kasa ba, abin da bai iya biyan bukatun dukkanin nakasassu da tsoffi, don haka, za a yi kokarin warware wannan matsala cikin lokaci don baiwa musu yanayin zama mai kyau. (Amina)