Bisa ayyukan sufuri da kwamitin ya gudanar tun daga shekarar 2014 zuwa 2015,da ya shafi hanyoyin jiragen kasa, hanyoyin motoci, hanyoyin ruwa, filayen jiragen sama da dai sauransu, yawansu ya kai 203, kana yawan sabbin ayyukan gina hanyoyin jiragen kasa a shekarar 2014 ya kai 66.
Ya zuwa karshen shekarar 2014, tsawon hanyoyin jiragen kasa mafi sauri a kasar Sin ya kai kilomita dubu 15.8, wanda ya kai matsayin farko a duniya. Kana an gaggauta gina hanyoyin jiragen kasa a tsakanin birane, da hada da ayyukan more rayuwa a tsakanin Sin da kasashe ko yankuna dake makwabtaka da ita, ta haka an kafa tsarin sufuri mai inganci a matakin farko. (Zainab)