Hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin ta ba da labari cewa, za ta sa kaimi ga wasu aikin gina manyan ababen more rayuwa ta fuskar zirga-zirga a wannan shekarar da muke ciki.
An ba da labari cewa, hukumar ta kebe kudi da ya kai kudin Sin yuan biliyan 34 daga kasafin kudi don gina manyan ababen more rayuwa ta fuskar zirga-zirga a shekarar 2014 da ta gabata, ya zuwa karshen shekarar 2014, tsawon layin dogon da ake aiki da su a kasar ya kai kilomita dubu 110, yayin da adadin ya kai kilomita miliyan 4.46 ta dogon hanyoyin motoci. Ban da haka kuma, yawan tasoshin jiragen ruwa ya kai 2116, yayin da yawan filayen saukar jiragen sama ya kai fiye da 202. Haka kuma, an shimfida layukan dogo a cikin birane 21 a nan kasar Sin, da tsawonsu ya kai kilomita 2800. Bugu da kari, tsawon hanyoyin jiragen kasa masu saurin tafiya ya kai kilomita dubu 15.8 wanda ya kai matsayin farko a duniya, wadanda suka shafi larduna da birane 28 a kasar.
A cikin wannan sabuwar shekara ta 2015, kwamitin zai mai da hankali sosai wajen tabbatar da wasu manyan ayyuka a yankin tsakiya da yammacin kasar, ciki hadda shimfida hanyoyin jiragen kasa da na motoci da sauransu. (Amina)