Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ce ta bayyana hakan yau yayin taron manema labarai a nan birnin Beijing.
Ta ce, Sin na fatan Japan za ta waiwayi tarihi kan irin abubuwan da ta aika a baya ba tare da wata rufa-rufa ba, sannan ta amince kan abubuwan da ta aikata wanda haka ne kadai zai sa Japan din ta samu wata makoma mai haske.
Madam Hua ta kuma bukaci Japan da ta yi la'akari kan sassan soja da tsaro a lokacin da take aiwatar da wadannan gyare-gyare sannan ta kasance mai bin turbar neman ci gaba cikin lumana da bunkasuwar yankin baki daya.
A jiya ne firaminista Abe a lokacin da yake jawabi a majalisar dokokin kasar ya jaddada shirinsa na yin gyaran fuska ga bangarorin aikin gona, ayyukan kiwon lafiya, shirin samar da tsaron jama'a, Ilimi da kuma tattalin narziki, sai dai bai yi bayani game da batun dokar tsaron da ake saran za a tattauna a zaman majalisar na wannan shekara ba. (Ibrahim)