Dangane da hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da Amurka kan aikin yaki da cin hanci, da kuma ko kasashen biyu za su kulla wata yarjejeniyar tusa keyar masu laifi, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yau a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin shawarwari da kasar Amurka kan wannan lamari, domin gano karin hanyoyin da suka dace wajen yaki da wannan matsala.
Ta ce, Sin da Amurka suna gudanar da shawarwari da hadin gwiwa a tsakaninsu kan wannan batu bisa tsarin APEC cikin yanayi mai kyau, kuma kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwarta da sauran mambobin APEC kan aikin yaki da cin hanci da karbar rashawa da dawo da kudaden da aka sata. (Maryam)