in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon jami'in diplomasiyyar Sin ya zargi Amurka da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin
2015-02-05 15:37:29 cri

Wu Zurong, tsohon karamin jakadan kasar Sin a birnin Houston na kasar Amurka, ya ce da gangan kasar Amurka ta amince Dalai Lama ya halarci karin kumallo na Addu'oin musamman da aka gudanar a Amurka a ranar Alhamis din nan.

Mr. Wu ya ce taron da Dalai Lama ya halarta tare da shugaba Barack Obama, wani mataki ne da Amurka ta dauka na tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin bisa hujjar kariya ga addini. Kana hakan tamkar nuna adawa ne ga manufar kasar Sin ta bin addinai cikin 'yanci, matakin da zai iya gurgunta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Wu Zurong wanda ya yi wannan tsokaci a jaridar Beijing Daily ta ranar 4 ga watan nan, ya kara da cewa wannan mataki da Amurka ta dauka, ko da yake ba a cika ganin irinsa ba, a hannu guda yana da nufin daga matsayin Dalai Lama, akwai kuma wasu sauran dalilai masu alaka da siyasa da kuma diplomasiyya.

Mr. Wu ya kuma ce kasar Amurka tana kauda kai ga ci gaban sha'anin addinai a kasar Sin, da kuma yadda Sinawa masu bin addinai suke gudanar da harkokin addinai bisa doka cikin 'yanci, amma a sa'i daya tana zargin Sin ba tare da wani sahihin dalili ba.

Ya ce Amurka ba ta taba tambayar kan ta game da ra'ayinta na nuna bambancin ma'auni, wajen girmama, da kulawa da masu bin addinin Musulunci ba, musamman a fannin kimanta yanayin da sauran kasashe ke ciki ta fuskar addini. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China