Wang Hong ya yi wannan bayani ne a yayin taron nazartar harkokin teku a kasar. Mr. Wang ya kara da cewa a wannan shekara, an samu kyautatuwar tsarin sana'o'i game da albarkatun teku, inda wasu sana'o'in gargajiya suka samun farfadowa, kana wasu sana'o'in da ke da alaka da hako gas, da albarkatun mai a teku suka gudana yadda ya kamata.
Banda wannan, saurin karuwar sana'ar hada-hadar magani daga halittun teku ke ci gaba da daukar matsayin farko, baya ga sana'ar kere-keren na'urori, da suka shafi ayyukan teku da ita ma ke samun saurin bunkasuwa.
Bugu da kari fannin sana'ar da kudi mai alaka da harkokin teku na samun daukaka sannu a hankali, ta yadda hakan ke samar da goyon baya ga tattalin arzikin da ya shafi harkokin teku. (Bilkisu)