A cewar Mr. Liao, hakan ya alamanta ci gaban da kasar ta Sin ta samu a fannin sanya hannun cikin tsarin dokokin tattalin arzikin duniya.
Liao Tizhong wanda ya bayyana hakan a gun taron manema labarai da cibiyar nazarin harkokin haraji ta duniya ta kasar Sin ta shirya, dangane da "manyan harkokin haraji guda 10 na duniya a shekarar 2010", ya kara da cewa, dokokin haraji na duniya suna da muhimmin matsayi a fannin dokokin tattalin arzikin duniya.
Yace a yayin da take sa hannu cikin harkokin tsara dokokin haraji na duniya, kasar Sin tana kuma mai da hankali a kan tabbatar da adalci, da kuma taimaka wa kasashe masu tasowa, da masu karamin karfi wajen shiga aikin inganta kwarewarsu ta fannin gudanar da harkokin haraji.
"Dole ne a yi la'akari da moriyar kasashe masu tasowa, da ma masu karancin kudin shiga, ya kamata a taimakawa juna, da hada kai da juna, domin tabbatar da jituwa a duniya.", in ji Liao Tizhong.(Lubabatu)