rukuni na farko na ma'aikatan tawagar tuni sun tafi cibiyar kungiyar AU dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha a karshen shekarar da ta wuce, kuma kasar Sin na shirya kafa sassan kula da harkokin siyasa, tattalin arziki, al'adu da tsaro da dai sauransu cikin tawagar wakilan kasar da ta tura a kungiyar, domin sa kaimi ga hadin gwiwar kasar Sin da kungiyar AU bisa fannoni daban daban, shugaba Kuang Weilin ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaran da aka yi a yau Alhamis 5 ga wata.
Ya kara da cewa, karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar da kasashen Afirka shi ne babbar manufar diflomasiyya ta kasar Sin. Kungiyar AU na taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar kasashen Afirka kan yin hadin gwiwa, da kuma taimakawa kasashen wajen samun ci gaba tattalin arziki da zaman takewar al'umma, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaron nahiyar, haka kuma tana taimaka matuka wajen ciyar da yunkurin dunkulewar kasashen Afirka gaba.
Kafuwar tawagar wakilan kasar Sin a kungiyar AU wani muhimmin al'amari ne mai ma'ana a huldar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar AU, wadda za ta inganta dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Don haka kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kungiyar AU domin ci gaba da bunkasa dangatakar hadin gwiwa dake tsakanin bangarorin biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi. (Maryam)