Li Yuanchao ya bayyana cewa, yanzu dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu ta shiga wani sabon yanayi. Yana fatan kasashen biyu za su aiwatar da manufofin da shugabannin kasashen biyu suka tsara, da kara yin mu'amala da koyi da juna kan harkokin raya jam'iyyun kasashen biyu, don inganta dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu bisa fahimtar juna kan harkokin siyasa, samun moriyar juna a fannin tattalin arziki, yin mu'amala kan al'adu da kuma taimakawa juna.
A nasa jawabin, Mantashe ya bayyana cewa, jam'iyyarsa ta ANC tana son koyi da fasahohin Sin a fannonin inganta karfin tafiyar da harkokin kasa, da sa kaimi ga yin kwaskwarima da dai sauransu. (Zainab)