in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi maraba da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a taron Minsk
2015-02-13 14:28:35 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyanawa 'yan jarida game da taron Minsk a ranar Alhamis 12 ga wata cewa, kasar Sin ta yi maraba da shugabannin kasashen Rasha, Jamus, Faransa, Ukraine su cimma daidaito tana kuma fatan tsammani cewa, wannan zai taimaka wajen sassauta hali mai tsanani a yankin gabashin Ukraine da kuma warware rikicin kasar Ukraine ta hanyar siyasa.

Hua Chunying ta bayyana cewa, a ganin kasar Sin, hanyar siyasa ce hanya daya kawai wajen warware rikicin. Don haka take fatan bangarori daban daban za su cika alkawarinsu da aiwatar da yarjejeniya yadda ya kamata don cimma zaman zaman lafiya a kasar Ukraine cikin hanzari. Kuma a nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen warware rikicin kasar Ukraine ta hanyar siyasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China