A ranar 3 ga wata da safe ne, a matsayinsa na shugaban kwamitin sulhu na watan Febrairu, Liu Jieyi ya shugabanci taron kwamitin, daga baya ya gudanar da taron manema labaru, inda ya yi bayani kan ayyukan kwamitin na wannan wata. Liu Jieyi ya ce, kwamitin sulhun zai gudanar da taruruka fiye da 20 a watan Febrairu, wadanda suka shafi batutuwa kimamin 20, kana za su tattauna kan batutuwan da suka fi jawo hankalin kasashen duniya da ke faruwa a Syria, Gabas ta Tsakiya, Iraki, Yemen, Guinea Bissau, Somaliya, Sudan ta Kudu da dai sauransu.
Ban da wannan kuma, Liu Jieyi ya bayyana cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 70 da kafa MDD da nasarar yaki da fascist a duniya. Don haka, kasar Sin ta yi kira da a gudanar da muhawara a tsakanin ministocin kasashe mambobin kwamitin sulhun bisa taken "tabbatar da zaman lafiya da tsaro, da duba tarihi da koyi da fasahohi da kuma jaddada alkawarin da aka yi na martaba ka'idojin tsarin MDD", kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ne zai shugabanci muhawarar. (Zainab)