Wakilin musamman na babban sakataren MDD mai kula da harkokin yara da yake-yake Leila Zerrougui ne ya bayyana hakan yayin da ya kalli yadda aka cimma wannan yarjejeniya a ranar Talatar da ta gabata. Ya ce amfani da yara a tashe-tashen hankula yana da mummunan tasiri ga rayuwarsu,muddin ana bukatar gina makomar kasa, ya zama wajibi a kare su.
Manufar da ke kunshe cikin shirin, shi ne za a kare yara daga daukar su a matsayin sojoji da amfani da su da keta wasu abubuwa da suka sabawa doka a kowa ne lokaci, ciki har da lokutan da ake fama da tashe-tashen hankula ko rikici.(Ibrahim)