Janar Wamala wanda ya bayyana wa manema labaru hakan a gundumar Jinja ta Gabashin kasar Uganada a ranar Jumma'a, ya kara da cewa kasarsa ba ta fatan fara janye dakarunta kafin hakan, domin gudun barin kasar Sudan ta Kudun cikin mawuyacin halin rashin tsaro.
Wannan dai tsokaci na Wamala na zuwa ne biyowa bayan matsin lambar da gamayyar kasashen duniya ke wa Uganda kan ta janye sojojinta daga kasar, matakin da kasashen ke cewa zai taimakawa shirin da ake yi na girke dakarun hadin gwiwa.
A yayin taron da shuwagabannin yankin Gabashin nahiyar Afirka suka gudanar a ranar Alhamis ne dai aka yanke shawarar tura tawagar wanzar da zaman lafiyar hadin gwiwa ta PDF zuwa Sudan ta Kudu.
Tun dai cikin watan Disambar bara ne dai Uganda ta jibge rukunin farko na dakarun sojinta a kasar Sudan ta Kudu, matakin da ta ce ta dauka domin kare faruwar kisan kiyashi a kasar. Inda daga bisani kuma ta kara yawan sojin nata bisa bukatar gwamnatin kasar ta kasar Sudan ta Kudu. (Saminu Hassan)