Kakakin Majalisai dinkin duniya Stephane Dujarric ya fada a jiya Alhamis cewar, abokanan aikinsu wadanda ke kokarin samar da kayayyakin agaji na ci gaba da yin yarjejeniya da dukanin bangarorin domin samar da kayayyakin agaji, tare da kwato kaddarorin da aka yi kokarin tabbatar da tsaron lafiyar masu ba da kayayyakin agaji na cikin gidan kasar Sudan ta kudu da na kasashen ketare.
Kakakin na majalisar dinkin duniyar wanda ya yi jawabi a yayin wani taron manema labarai, bai bayar da karin bayani ba a game da yawan adadin mutanen da fadan ya tilasta masu ficewa daga muhallansu.
Jihar Jonglei na daya daga cikin jihohi goma a kasar Sudan ta kudu, kuma ita ce jiha mafi girma da yawan jama'a a jaririyar kasar. (Suwaiba)