in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mayakan Boko Haram 109 a kan iyakar Nijar da Najeriya
2015-02-07 16:35:30 cri
Rundunar sojin jamhuriyar Nijar, ta ce dakarunta sun samu nasarar harbe mayakan kungiyar nan ta Boko Haram su 109, yayin da kuma wasu sojojin kasar 4 suma suka rasa rayukansu, a wani dauki-ba-dadi da bangarorin biyu suka yi, daf da kan iyakar kasar da Najeriya.

Yayin harin na ranar Juma'a, wanda ya kasance na farko da mayakan kungiyar suka kai yankin kasar ta Nijar, sun yi yunkurin mamaye garuruwan Bosso da Diffa, garuruwan kan iyaka dake yankin kudu maso gabashin kasar.

Rahotanni sun ce dakarun hadin gwiwar Nijar da Chadi ne suka dakile farmakin 'yan Boko Haram din, kuma ya zuwa yanzu ba a bayyana rashin rayuka daga bangaren sojojin kasar Chadi ba. koda yake an ce musayar wutar ta ritsa da wani farar hula guda.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China