Ranar 7 ga wata, a birnin Yaounde, hedkwatar kasar Kamaru, kasashe mambobin kwamitin kasashen da ke kewayen tabkin Chadi da kuma kasar Benin sun sanar da kafa wata rundunar kasa da kasa mai kunshe da sojoji 8700 domin yaki da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Boko Haram.
A wannan rana, wadannan kasashe sun kawo karshen taron kwararru na tsawon kwanaki 3 a Yaounde. A yayin rufe taron, wakilan kasashen Kamarun, Nijeriya, Nijar, Chadi da Benin sun sanar da shirin kafa wannan runduna.
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa 'yan jarida cewa, wannan runduna za ta hada sojojin Nijeriya 3250, sojojin Chadi 3000, sojojin Kamarun 950, sojojin Nijar 750 da sojojin Benin 750.
A 'yan kwanankin baya, kungiyar Boko Haram ta kai hare-haren ta'addanci da dama, lamarin da ya sa fararen hula mazauna yankunan arewacin Nijeriya sun gudu zuwa kasashen Kamaru, Chadi da Nijar. Har wa yau kuma 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hare-hare da dama a arewacin kasar Kamarun da ke makwabtaka da Chadi.