in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude filin wasa da kasar Sin da sake ginawa a Ziguinchor na kasar Senegal
2015-02-21 16:55:05 cri
Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya kaddamar a ranar Jumma'a da bikin bude filin wasa na Aline Sitoe Diatta dake birnin Zinguichor dake kudancin kasar Senegal, da kasar Sin ta sake ginawa da sake gyaran shi bisa dalilin huldar dangantaka tare da kasar Sin. Tare da rakiyar mambobin gwamnati da jakadan kasar Sin da ke Senegal, Xia Huang, shugaban kasar Senegal ya samu tarbo daga miliyoyin mutane. Kungiyar wasannin motsa jiki ta Ziguinchor ta yi maraba da sake bude filin wasa na Aline Sitoe Diatta.

Jakadan kasar Sin, Xia Huang ya bayyana cewa bude wannan gini ya kasance cikamakin zagayen gina filayen wasanni goma sha daya a cikin jahohin kasar ne, bisa jimillar kudin Sefa biliyan 25.2.

Sake gina wadannan filayen wasanni 11 a jahohin kasar na nuna wani sabon salon dangantakar abokantaka da ke tsakaninmu in ji jakadan kasar Sin.

A nasa bangare, shugaba Macky Sall ya nuna godiya ga kasar Sin, tare da jinjinawa huldar dangantaka da ke tsakanin Sin da Senegal da kuma ke ci gaba da karfafa a kowa ce rana bisa turbar abokantaka da dangantaka mai armashi. Haka kuma ya yi kira ga al'ummomi da mutanen da aka dorawa nauyin kula da wannan gini da su nuna azama wajen bada kulawa ga wannan abu mai daraja. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China