in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Senegal ya gana da tawagar JKS
2014-05-14 10:35:32 cri
Shugaban kasar Senegal kuma jagoran jam'iyyar APR Macky Sall, ya gana da tawagar sada zumunta ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, karkashin jagorancin Yu Hongjun mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin cudanya da ketare na kwamitin tsakiyar JKS.

Yayin ganawar tasu a jiya Talata 13 ga wata a birnin Dakar, Mr. Yu ya bayyana cewa, jam'iyyar JKS na mayar da hankali kan bunkasa dangantakar dake tsakaninta da jam'iyyu daban daban na kasar Senegal, ciki har da APR.

Haka nan Sin na fatan ganin an karfafa cudanya tare da jam'iyyun, don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a duk fannoni gaba.

A nasa bangaren, shugaba Sall ya bayyana cewa, jam'iyyarsa na fatan koyon fasahohin raya jam'iyya, da JKS ta samu, musamman ma ta fuskar ladabtarwa, matakin da ya ce zai taimaka wajen karfafa hadin kai, da dinkewar jam'iyyar. Baya ga karfafa matsayinta a fagen jagorancin kasar ta Senegal. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China