in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada sabon firaministan kasar Senegal
2014-07-07 15:02:48 cri

A jiya Lahadi ne aka bayyana nadin ministan farfado da tattalin arziki na kasar Senegal Mohammed Dionne, a matsayin sabon firaministan kasar, domin maye gurbin tsohuwar firaministar kasar Aminata Toure, wadda aka sallame ta sakamakon gaza lashe zabukan da suka gabata a kasar.

Tuni dai fadar shugaban kasar ta Senegal ta tabbatar da wannan batu.

A wani gajeren jawabin da ya yi ga kafofin watsa labarai, Mr. Dionne ya yi kira ga jama'ar Senegal da su yi kokari, wajen ganin an cimma burin farfado da kasar, kamar yadda shugaba Macky Sall na kasar ya gabatar. Haka zakila, ya nanata babban burin shugaba Sall na ganin an aiwatar da manufofin raya ayyukan gona, yana mai cewa, gwamnatinsa za ta kara himma wajen marawa habakar karin sana'o'i baya, da nufin bunkasa samar da guraban ayyukan yi.

Rahotanni sun ce Mr. Dionne, ya riga ya kafa sabuwar majalisar ministoci jim kadan da kama aiki, mai ministoci 30 da kuma wakilai uku da ke da matakin minista.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China