in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai makoma mai haske game da hadin gwiwa tsakanin Sin da Senegal, in ji shugaban kasar Senegal
2014-02-25 16:01:40 cri

Shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya shedawa manema labaru a ran 24 ga wata cewa, kwanakin baya ya kai ziyara mai muhimmanci kasar Sin, inda ya yi musayar ra'ayi da shugabannin kasar kan harkokin da suka shafi hadin gwiwar kasashen biyu.

Mr. Sall ya bayyana cewa, a yayin ziyararsa, ya yi shawarwari da shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping, wanda a cewarsa, Sin na nuna goyon baya ga Senegal kan kokarin da take na bunkasa tattalin arzikinta. Ban da haka, akwai makoma mai kyau ga bangarorin biyu wajen yin hadin gwiwa a fannin yawon shakatawa, kuma Sin na fatan mai da kasar Senegal matsayin wani wuri da Sinawa za su rika zuwa domin yawon shakatawa.

Dadin dadawa, Sall ya ce, kasarsa ta kammala wasu ayyuka da dama da taimakon kasar Sin, abubuwan da suka samu matukar karbuwa daga mutanen kasar.

Bugu da kari, a dai wannan rana shugaba Sall ya jagoranci wani taro tsakanin masu zuba jari ga bunkasuwar tattalin arzikin Senegal a birnin Paris, inda ya gabatar da shirin raya Senegal.

A cikin wata sanarwa daga fadar gwamnatin kasar, an bayyana cewa, yawan kudin da wadannan kasashe suka yi alkawarin zubawa kasar, ya kai dala biliyan 7.5, wanda ya haura ainihin abin da gwamnatin ta bukata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China