in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin bude asibitin yara a kasar Senegal da kasar Sin ta taimaka
2014-01-20 10:55:46 cri
A ranar 18 ga wata, a sabon gundumar Diam Niadia da ke da nisan kilomita 45 da Darkar, hedkwatar kasar Senegal ne, aka yi bikin bude asibitin yara a kasar da Sin ta taimaka wajen gina shi. Shugaban kasar Senegal Macky Sall da firaministar kasar Aminata Touré sun halarci bikin.

Shugaban Sall ya ce, bangaren kiwon lafiya yana cikin muhimmin sashin da gwamnatin Senegal za ta mayar da hankalin a kai, ya kuma jinjina goyon baya da kasar Sin da ta dade tana baiwa kasar. A matsayin wani babban ci gaba cikin hakikanin hadin gwiwar bangarorin biyu, asibitin yaran da Sin ta taimaka na da fasahohin zamani, kuma dukkan yankunan Darkar da Thies za su iya cin moriyar shi, matakin da zai kyautata harkokin kiwon lafiya na kasar, da kawo alheri ga jama'ar kasar.

A gun bikin bude asibitin, jakadan Sin a kasar Senegal Xia Huang ya ce, hadin gwiwa a fannin kyautata zaman rayuwar jama'a wani muhimmin kashi ne cikin hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Kasar Sin tana dukufa ka'in da na'in wajen raya aikin kiwon lafiya a kasar Senegal, ya zuwa yanzu, Sin ta tura kungiyoyin ba da aikin jinya 15 zuwa kasar, wadanda suka ba da babbar gudummawa wajen kyautata lafiyar jama'a da sha'anin kiwon lafiya na kasar. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China