in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi zanga zangar nuna adawa da mujallar Charlie Hebdo a Senegal
2015-01-18 16:57:00 cri

A wannan rana da yamma, bayan an kawo karshen sallar Jumma'a a ranar 16 ga wata, duban musulmai sun fito kan titunan birnin Dakar na kasar Senegal don bayyana matukar adawa da zanen mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta yi na wulakanta manzon Allah (SAW) Annabi Mohammed. Masu zanga-zangar sun yi tattaki har zuwa ofishin jakadancin kasar Faransa domin nuna rashin jin dadinsu tare da kone tutar kasar Faransa. Shugaban wata kungiya mai zaman kanta Jibril Touré ya ce, fadi albarkacin baki, ba ya nuna cewa wuce gona da iri ko kadan, musamman ma a kan addini. 'Yan sandan dai sun yi amfani da barkonon tsofuwa domin tarwatsa masu zanga zangar.

A wannan rana kuma, shugabannin addinai daban daban na kasar Senegal sun bada sanarwa domin yin tir da matakin takalar musulmai da mujallar Charlie Hebdo ta yi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China