Ana dai sa ran gudanar wannan biki ne ya zuwa ranar 30 ga watan nan na Nuwamba, inda mahalartansa za su gamewa idanunsu kayayyaki na musamman masu alaka da al'adun kasashe membobin kungiyar kasashe renon Faransa.
Firaministan kasar ta Senegal Mohamed Abdallah Dionne ne dai ya gabatar da jawabin bude bikin nune-nunen. Bikin da aka yiwa lakabi da "yin amfani da fasahohin sadarwa na zamani don sa kaimi ga bunkasa kasa, da al'adun kasashe a fannoni daban daban".
Shi ne kuma kashin da ya shafi nune nunen al'adun gargajiya a taron kolin kungiyar ta kasashe masu amfani da harshen Faransanci na wannan lokaci. (Zainab)