Shugaba Sall ya kara da cewa, tun lokacin kasashen biyu suka farfado da dangantakar diplomasiyya a shekarar 2005, suka samu ci gaba mai armashi wajen yin hadin kai.
Ya bayyana cewa kasar Sin ta dade tana tura runkunonin jiyya da masanan kimiyya a fannin sha'anin noma zuwa kasar Senegal, ban da haka, ta taimakawa kasar wajen gina wasu filayen wasanin motsa jiki, manyan ababen more rayuwan dan adam, alal misali, gyara da habaka filayen wasan motsa jiki 11. Babban dakin wasan kwakwaiyo na Dakar da wani kamfanin kasar Sin ya gina ya kasance daya daga cikin gine-gine mafi kyau a nahiyar Afrika, ban da haka, an fara gina dakin nuna kayayyakin gargajiyar kasar da kasar Sin ta taimaka wajen gina shi.
Game da wasan kwaikwayon da ma'aikatan gidan rediyon kasar Sin suka fassara zuwa yaren Senegal kuma wasu 'yan wasan kwaikwayon kasar Senegal suka sanya murya a ciki mai suna "Doudou da surukanta", wanda a yanzu haka ya yi farin jini sosai a kasar, shugaba ya ce, al'adu mafari ne kuma karshen kome da kome, wannan wasan kwaikwayo wanda ya shahara sosai ya shaida cewa, jama'ar kasashen biyu za su samu ci gaba mafi kyau ta hanyar yin hadin gwiwa a fannin al'adu nan gaba. (Amina)