Wannan mataki ya fito daga bakin sakatare janar din ma'aikatar dake kula da harkokin mata da iyali ta kasar Senegal, mista Adama Baye Racine Ndiaye yayin bikin ranar yaki da kaciya ta kasa da kasa da ta gudana a ranar Jumma'a.
Al'adar yin kaciya na ci gaba da zama ruwan dare a kasar Senegal, duk muhimman kokarin da gwamnatin kasar ta yi tare da taimakon kungiyoyin fararen hula, in ji wannan jami'i.
Yin watsi da wannan al'adar kaciya na bukatar hadin gwiwar dukkan bangarori daban daban na kasa, in ji mista Ndiaye, tare da jaddada niyyar gwamnatin kasar Senegal wajen kara bada goyon baya, kare mata da kananan 'yan mata da wadannan munanan al'adu.
A cewar wakiliyar asusun kula da al'umma na MDD dake kasar Senegal, madam Andrea Wojnar Diagne, kananan 'yan mata da mata fiye da miliyan 130 suka fuskanci wasu tabi'un dake lalata al'aurar mata kana a kowace shekara kimanin 'yan mata miliyan 3 ake ma kaciya.
A nahiyar Afrika, kimanin mata da 'yan mata miliyan 92 aka yi ma kaciya, kuma yawanci tun daga bakin shekaru goma, in ji madam Diagne tare da bayyana cewa a kasashe 29 na Gabas ta Tsakiya da Afrika, musammun ma a yammacin Afrika wannan al'ada ta fi kamari. (Maman Ada)