Gwamnatin kasar Senegal ta rufe iyakarta da kasar Guinea, a kokarin ta na kandagarkin yaduwar kwayoyin cutar Ebola da aka bada rahoton bullarta a kasar ta Guinea.
Bisa sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Senegal ta fitar a jiya Asabar, Senegal din ta yanke shawarar rufe iyakarta a yankin Kolda, da Kedougou da dai sauran yankuna dake makwabtaka da Guinea. Sanarwar ta ce, mahukunta a wadannan yankuna sun riga sun dauki matakin aiwatar da hakan.
Rahotanni dai sun bayyana cewa, kwayoyin wannan cuta ta Ebola na yaduwa cikin sauri yanzu haka a kasar ta Guinea, wadda ke yammacin nahiyar Afrika. Inda ya zuwa ranar Alhamis din da ta gabata, mutane 103 suka kamu da cutar, kuma tuni 66 daga cikinsu suka rasu. Hakan dai ya sanya wasu kasashen Afrika gaggauta daukar matakan kandagarkin tsllakawar cutar zuwa nasu kasashe.
Cutar Ebola, na cikin cututtukan dake saurin hallaka Bil Adam, wadda kuma ke iya yaduwa cikin sauri. Kana kawo yanzu babu maganin ta. Cutar da kan bi jini da sauransu ruwan jiki, na iya hallaka al'umma da dama cikin kankanen lokaci. Wadanda kuma suka kamu da ita, kan yi fama da zazzabi, da ciwon kai, gudawa, da amai da sauransu. (Amina)